DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mata ta saki mijinta saboda ya ki gyaro wayarta da darajarta ta kai N70,000 da ta lalace

-

Wata matar aure mai suna Zainab Alhassan ta saki mijinta, Tijjani Muhammad, saboda kin gyara wayarta da ta lalace da darajarta ta kai Naira 70,000.

Zainab ta shaida wa kotu cewa ta gaji da zaman auren, don haka tana son ta rabu da mijinta ta hanyar Khul’i – wato irin saki da mace ke maido wa mijinta sadakinta domin ta samu ’yancinta.

Google search engine

Ta ce tana shirye ta mayar da sadaki na N30,000 da ta karɓa domin a sake ta daga auren. Zainab ta bayyana cewa tana kallon fim a wayarta lokacin da mijinta ya fara faɗa da ita, ya kwace wayar ya buga ta a kasa, ta lalace. Sai dai ta ce ba ta da wata shaida da za ta tabbatar da ikirinta.

Shi kuma mijin, Tijjani Muhammad, ya ce bai da matsala da bukatar sakin da matarsa ke nema, amma ya musanta zargin cewa shi ne ya lalata wayar.

Alkali Mu’awiyya Shehu ya raba auren bisa tsarin Khul’i, inda ya amince da sakin amma ya ƙi amincewa da bukatar matar ta biya ta farashin wayar da ta ce mijinta ya lalata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara