Wani lauya mai suna Johnmary Jideobi ya garzaya babbar kotun Abuja yana neman ta hana tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Jideobi ya kuma nemi kotun da ta hana hukumar zaben Nijeriya amincewa da sunan Jonathan a matsayin dan takara.
A cikin bayanan da ya shigar, ya bayyana cewa, Jonathan ne ya karasa wa’adin mulkin marigayi Umaru Musa ‘Yar’adua daga bisani kuma ya yi shekaru 4 bayan lashe zaben 2011 wanda hakan ya karar da wa’adi biyu da kundin tsarin mulki ya yi masa tanadi, kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.