Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya amince da karrama mutane 959 da lambar girmamawa ta ƙasa a zaman majalisar kolin kasar da ya wakana a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Babbar sakatariyar ofishin harkokin ministoci, Dr. Emanso Umobong, ta ce, an zaɓi mutane 824 don karramawar 2024/2025 da kuma wasu 135 na musamman wanda adadin ya kai 959 gaba ɗaya kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Umobong ta kara da cewa, wadanda aka karrama sun haɗa da fitattun ‘yan Nijeriya da wasu daga ƙasashen waje da suke ba da gudummawa a fannoni daban-daban, ciki har da Bill Gates, tawagar ‘yan kwallon kafa ta mata, Super Falcons, da na kwando, D’Tigress da kuma Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC wanda ya sauka daga mukaminsa a cikin kwanakin nan.