Shugaban Nijeriya Bola Tinubu zai halarci taron zuba jari na ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje karo na takwas a matsayin bako na musamman, wanda za a gudanar daga ranar 11 zuwa 13 ga watan Nuwamban 2025 a Abuja.
Shugabar hukumar kula da ’yan Nijeriya mazauna ƙetare ‘NiDCOM’ Abike Dabiri-Erewa ce ta sanar da hakan yayin taron manema labarai kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Abike ta ce tun bayan fara taron a 2018, an samu karuwar zuba jari daga ’yan Nijeriya da ke ƙasashen waje a fannoni kamar gidaje, kiwon lafiya, noma, fasahar sadarwa, makamashi, masana’antu da harkokin kirkire-kirkire.
Dabiri-Erewa ta kara bayyana cewa, a taron bara na 2024 an cimma yarjejeniyar zuba jari da ta kai kimanin naira miliyan 673 a fannoni daban-daban.