Wani sashe na sojin ƙasar Madagascar ya sanar da cewa ya karɓe ikon ƙasar baki ɗaya, abin da shugaban ƙasar Andry Rajoelina ya bayyana a matsayin yunƙurin karɓar mulki ta hanyar da ba ta dace ba.
Jaridar Punch ta rawaito cewa lamarin ya zama sabon salo cikin zanga-zangar da ta yi akalla makonni biyu ana yi a ƙasar saboda matsalolin wutar lantarki da ruwan sha.
A ranar Lahadi, Shugaban kasar Rajoelina ya tabbatar da cewa ana ƙoƙarin yin juyin mulki ta hanyar da ba ta dace ba, yana mai kiran ‘yan ƙasa da su zauna lafiya tare da shiga tattaunawa domin warware rikicin da ke addabar ƙasar.
Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 22 ne suka rasa rayukansu tun bayan barkewar zanga-zangar a ranar 25 ga Satumba, sakamakon harbin jami’an tsaro.



