Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC, inda ya bayyana cewa matakin nasa na da nufin kara inganta ci-gaban jihar da kasa baki daya.
Mbah ya sanar da haka ne a taron manema labarai da ya gudana a birnin Enugu a ranar Talata, yana mai cewa ya yanke shawarar ne bayan dogon tunani da tattaunawa da abokan aiki domin samun dama ta hadin gwiwa da ci-gaba.
A cewarsa, ya shiga jam’iyyar APC ne saboda hangen nesa na samun sauyi da ci-gaba, yana mai jaddada cewa jam’iyyar za ta ba da ingantaccen dandali na aiwatar da manufofin ci-gaban jihar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Gwamnan ya samu rakiyar tsohon gwamna, Ifeanyi Ugwuanyi da wasu ‘yan majalisu na jiha da tarayya, inda ya ce sauyin jam’iyyar ba abu ne da aka yi da sauki ba, amma wajibi ne domin hidimtawa al’ummar Enugu yadda ya kamata.



