Jam’iyyar ADC ta zargi shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin juya Nijeriya zuwa kasa mai amfani da jam’iyya ɗaya, bayan ficewar wasu gwamnonin jihohi daga jam’iyyun adawa zuwa APC.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya fitar, ya ce sauya sheƙar gwamnonin Enugu da Bayelsa zuwa jam’iyyar mai mulki ya tabbatar da abin da ADC da sauran jam’iyyun adawa ke faɗa tun da farko cewa ana ƙulla makirci don murƙushe dimokuraɗiyya a Nijeriya.
Bolaji ya ce sauyin jam’iyya ba zai dame su ba, domin a cewarsa, gwamnonin sun bar mutanensu don haɗa kai da jam’iyyar da ta jefa mafi yawan ‘yan Nijeriya cikin kangin talauci.
Ya kara da cewa gwamnatin APC ta gaza wajen tsaro, tattalin arziƙi, kiwon lafiya, da yaki da cin hanci, sannan ta lalata martabar ƙasar a idon duniya.
A cewarsa lokacin da jama’a ke wahala, abin da ake bukata shi ne jam’iyyun adawa su tashi tsaye su kare dimokuraɗiyya da rayuwar talakawa, amma wasu shugabanni sun zabi bin bin masu mulki saboda son zuciya,kuma a zaben 2027 zai banbance tsakanin gaskiya da karya.