Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya bukaci gwamnati da ta yi doka domin daidaita amfani da kafafen sada zumunta a Nijeriya saboda yadda ake amfani da su wajen yada maganganu marasa ladabi da suke haddasa fitina.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Sarkin ya bayyana hakan ne ta bakin Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, yayin taron koli na malaman Arewa kan matsalar tsaro da tattalin arziki da kungiyar malaman Arewa ta shirya a Kaduna.
Ya ce rashin kula da kafafen sada zumunta na iya jefa kasar cikin tashin hankali da rikice-rikicen kabilanci da addini.
A cewarsa, yanzu kowa na iya zagin shugaba, malami ko mutane masu kima da mutunci ba tare da hukunci ba.
A wasu ƙasashe ana bin diddigin duk wanda ya yada kalaman da ke tada fitina, ana kuma hukunta shi, kamata ya yi a yi irin haka a Nijeriya.