Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Kano, ta kori dalibai 34 bayan an same su da laifin satar amsa a jarabawa, ta kuma dakatar da wasu mutum 13 na zangon karatu guda.
Hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na jami’ar, Malam Abdullahi Datti, ya fitar ranar Juma’a.
Jaridar Punch ta rawaito cewa sanarwar ta ce hukuncin ya biyo bayan amincewar jami’ar kan rahoton kwamitin da ke binciken karya dokar jarabawa da ya gabatar.
Datti ya ce kwamitin ya bayar da shawarwari daban-daban ga ɗaliban da aka samu da laifukan, ciki har da gargadi ga wasu da ba a kora ba.