Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya ce manufofin tattalin arziƙin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bijiro dasu sun taimaka wajen farfaɗo da tattalin arziƙin Nijeriya.
Uzodimma ya bayyana haka ne a taron Gwamnonin jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Juma’a a jihar Kebbi, inda ya ce lokacin da Tinubu ya hau mulki a 2023, kasar ta kusa durkushewa.
Ya ce shugaban kasar ya gano cutar da ke kokarin durkusar da Nijeriya tare da ɗaukar matakan da suka hada da cire tallafin man fetur da aiwatar da wasu sabbin tsare tsare a bangaren kudi, abin da ya taimaka wajen dawo da kasar daga halin rashin tabbas tare da ci gaba da samun arziki mai tarin yawa.