Kamfanin matatar mai ta Dangote ya bayyana cewa tun bayan da matatar man da ke fitar da ganga 650,000 a rana ta fara aiki, aƙalla sau 22 aka yi yunƙurin lalata kayayyakin aiki ko hana ta gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Mataimakin shugaban kamfanin mai kula da sashen mai da iskar gas, Devakumar Edwin ne ya bayyana hakan a yayin da tsohon mai taimakawa shugaban ƙasa Reno Omokri ya kai ziyarar gani da ido zuwa matatar da ke Lekki, a jihar Legas.
Edwin ya ce duk waɗannan hare-haren an shawo kansu cikin nasara saboda tsarin tsaro na zamani da matatar ke amfani da shi.
Rahotannin da Daily Trust ta ruwaito sun nuna cewa, matatar ta fuskanci sauye-sauyen ma’aikata da suka shafi kusan mutum 800, wanda hakan ya janyo yajin aiki daga kungiyar manyan ma’aikatan mai da iskar gas ta PENGASSAN, kafin gwamnati ta shiga tsakani aka dakatar da yajin aikin.
Edwin ya kuma karyata jita-jitar da ke cewa matatar tana fama da matsalolin aiki ko na samun danyen mai, yana mai cewa wadannan bayanai ba gaskiya ba ne, illa wani yunƙuri na ɓata suna da nasarorin da kamfanin ke samu.