Sarkin Onitsha, Igwe Nnaemeka Achebe, ya caccaki ‘yan siyasa bisa mayar da hankali kan siyasa maimakon gudanar da mulki yadda ya kamata tun kafin zaben 2027.
Achebe ya bayyana haka ne yayin wani bikin gargajiya da aka gudanar a jihar Anambra, inda ya nuna damuwarsa kan yadda gwamnoni da ‘yan majalisa ke tsunduma cikin harkokin siyasa maimakon magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar ‘yan Nijeriya.
A cewarsa, irin wannan hali na nuna yadda wasu shugabanni suka fi son kare muradunsu na siyasa fiye da jin daɗi da walwalar jama’a da ci-gaban ƙasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Obi Achebe ya yi kira ga shugabanni a Nijeriya su mayar da hankali kan gudanar da aiki cikin gaskiya da rikon amana, tare da cewa abin da al’umma ke bukata yanzu shi ne shugabanci nagari, ba yakin neman zaɓe kafin lokaci ba.