Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa lallai dukkan ɗalibai masu rubuta jarabawar kammala sakandare su cigaba da rubuta lissafi tare da harshen Turanci a matsayin wajibi.
Mai magana da yawun ma’aikatar ilimi ta Nijeriya Boriowo Folashade ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a Lahadinan.
A ranar Talata Boriowo ta sanar da cewa ɗaliban sashen fasaha da zamantakewa ba za a sake buƙatar lallai sai sun samu kiredit a lissafi ba kafin su samu gurbin karatu a jami’a ko kwalejin kimiyya sanarwar da ta jawo ce-ce-ku-ce tsakanin masana ilimi da jama’a.
Sai dai a sabon bayanin ta ce wannan gyara bai soke wajabcin ɗalibai su rubuta jarabawar lissafi da Turanci ba, illa dai ya ba jami’o’i damar karɓar ɗalibai zuwa wasu fannoni ko shirye-shiryen karatu da ba lissafi ko Turanci ke zama tilas ba.
A cewarta, wannan mataki na cikin shirin gwamnati na tabbatar da daidaito da ba kowa dama wajen samun ilimi, tare da bunƙasar ci-gaban ɗan Adam kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.



