DCL Hausa Radio
Kaitsaye

EFCC ta kwato kudade da kadarori na sama da Naira biliyan 500 – Kashim Shettima

-

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta karbo kadarori da kudade da darajarsu ta haura Naira biliyan 500.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin bude taron horaswa na kwanaki uku ga alkalai da manyan masana shari’a, wanda EFCC tare da Cibiyar Shari’a ta Ƙasa (NJI) suka shirya a Abuja.

Google search engine

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito ya ce, wannan ci gaba ya samu ne saboda Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba ta tsoma baki cikin ayyukan hukumar, abin da ya taimaka mata wajen samun nasara a yaki da rashawa.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa EFCC ta samu hukuncin laifuka guda 700 cikin shekaru biyu da wannan gwamnati ke mulki.

Shettima ya bayyana cewa kudaden da aka karbo daga hannun masu laifi ana amfani da su wajen aikin ci gaban ƙasa a sassa daban-daban na tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan sanda sun kama barawon da ya yi amfani da kakin NYSC don yi fashi a Enugu

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Enugu ta kama wani mutum da ake zargi da yin fashi da makami, ta hanyar basaja da kakin NYSC domin...

Hadurran mota a Najeriya sun yi sanadin rayuka fiye da 3000 a shekarar 2025 – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa akalla mutane 3,433 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 22,162 suka jikkata a cikin hadurra...

Mafi Shahara