Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta bayyana cewa akalla mutane 3,433 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu 22,162 suka jikkata a cikin hadurra 6,858 da suka faru a faɗin Najeriya daga watan Janairu zuwa Satumbar 2025.
Jaridar Punch ta ruwaito babban Kwamandan FRSC, Shehu Mohammed, ya bayyana hakan ne a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja, domin ƙaddamar da gangamin wayar da kan jama’a na watanni hudun karshen shekarar nan.
Ya ce yawancin hadurran sun samo asali ne daga gajiya yayin tuƙi, ɗaukar fasinjoji fiye da ƙima, ɗaukar mutane a motoci na kaya, da sauransu.
FRSC ta ce za ta ƙara tsaurara matakai ta hanyar sanya jami’ai da masu sa kai a manyan tituna, gudanar da binciken motoci kyauta, da kuma wayar da kai a tashoshin mota da tarukan jama’a.