Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga alkalai da sauran ma’aikatan shari’a a Najeriya da su ci gaba da zama masu gaskiya, adalci, da rashin cin hanci wajen aiwatar da shari’a.
Tinubu ya gargadi cewa rushewar kowace al’umma yana farawa ne idan masu fassara dokokinta suka zama masu karkata ko cin hanci.
Yayin bude taron bita na hukumar EFCC tare da Cibiyar Alƙalai ta Ƙasa (NJI) a birnin Abuja ranar Litinin, wanda mataimakinsa, Kashim Shettima, ya wakilce shi, Shugaba Tinubu ya ce ginshiƙin ɗabi’ar Najeriya yana ta’allaka ne da amincin tsarin shari’arta.
Ya ce gwamnatin sa tana ƙoƙarin inganta walwala da yanayin aiki na ma’aikatan shari’a, inda sabbin karin albashi da aka yi kwanan nan ke cikin matakan da ake ɗauka don ƙarfafa ikon shari’a mai zaman kanta.
Premium Times ta ruwaito Shugaban ya kuma tabo batun jinkirin shari’a a manyan shari’o’in cin hanci da rashawa, yana mai cewa akwai buƙatar inganta saurin yanke hukunci kamar yadda ake yi a shari’o’in zamba ta yanar gizo.