Jam’iyyar Labour party ta bayyana cewa ta hanyar hada kai ne kawai za a iya kawo karshen mulkin shugaban Nijeriya Bola Tinubu a 2027.
Tsagin jam’iyyar mai biyayya ga Peter Obi da Alex Otti, ya ce muddin tsohon mataimakin shugaban Nijeriya Atiku Abubakar zai ajiye burinsa na zama shugaban kasa ya kuma mara wa Peter Obi baya, cikin ruwan sanyi zai kayar da Tinubu a 2027, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cewar mai rikon kwaryar sakataren jam’iyyar na Nijeriya Prince Tony Akeni, wannan dama ce ga Atiku Abubakar na ceto kasar daga radadin rashin shugabanci na gari da take fama da shi.