Gwamnatin Nijeriya ta ce rundunar ‘yansanda, hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, tare da NDLEA mai yaki da sha da fatauci miyagun ƙwayoyi ne za su sake bibiyar jerin mutanen da shugaba Tinubu ya yi wa afuwa don tantance su.
Jaridar Punch ta ruwaito ministan shari’a na Nijeriya Lateef Fagbemi SAN na cewa daukar matakin wani yunkuri ne na tabbatar da gaskia da adalci a kan batun afuwar.
Labari mai alaka: Gwamnati Nijeriya tace haryanzu ba a saki kowa ba a cikin mutanen da Tinubu ya yiwa afuwa
Haka kuma shugaba Tinubu na jiran sakamakon da wadannan hukumomi za su fitar, don daukar matakan da suka dace.
Labari mai alaka: Ni na roki gwamnati da ta yafe ma Maryam Sanda – Mahaifin Bilyaminu Bello
Sai dai jaridar ta yi hasashen cewa akwai yiwuwar a cire fiye da rabin sunayen wadanda aka yi wa afuwar da zarar an kammala binciken.