Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU ta janye yajin aikin gargadin da ta tsunduma.
Shugaban kungiyar Farfesa Chris Piwuna ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Laraba, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Labari mai alaka: ASUU ba ta da hujjar shiga yajin aiki domin mun biya dukkanin bukatunta – Gwamnatin Nijeriya
A cewar sa, daukar matakin ya biyo bayan wani zama da kwamitin zartarwar kungiyar ya gudanar, bayan samun martani daga bangaren gwamnati kan bukatunsu.
Haka kuma, ASUU ta ce iyaye, dalibai da kuma kungiyar kwadago ta NLC sun taka rawar gani wajen sake bibiyar yajin aikin gargadin da ta yi niyyar gudanarwa na tsawon makonni biyu.