Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan na fuskantar matsin lamba daga manyan jiga-jigai na yankin Niger Delta da ke ƙoƙarin ganin ya janye kudirin sake neman kujerar shugaban ƙasa a zaben 2027, tare da mara wa Shugaba Bola Tinubu baya don tazarcensa.
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa tsohon jagoran ‘yan tawaye, Government Ekpemupolo, wanda aka fi sani da Tompolo, ne ke jagorantar wannan yunkuri na shawo kan Jonathan ya janye aniyarsa, tare da goya ma shugaba Tinubu baya a wa’adinsa na biyu.
Tompolo tare da abokansa da suka haɗa da shugaban Tantita Security Services Nigeria Limited, Kestin Pondi, da mataimakin dan takarar gwamnan APC a Bayelsa a 2023, Joshua Maciver, sun kai ziyarar sirri ga Jonathan a gidansa da ke Otuoke, ƙaramar hukumar Ogbia, ranar 16 ga watan Oktoba, 2025.
Rahotanni sun ce taron ya ɗauki sa’o’i da dama, wanda ya nuna muhimmancin batun.
Majiyoyi daga kusa da bangarorin biyu sun tabbatar da cewa ziyarar ba ta da nasaba da batun tsaro kamar yadda aka ruwaito a baya, illa dai tattaunawa ce ta siyasa da nufin ganin Jonathan ya mara wa Tinubu baya a zaben 2027.



