DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Nijeriya ta kubuta daga jerin kasashen da ake zargi da almundahanar kudade

-

Kungiyar FATF wadda ke yaki da zambar kudade a duniya ta cire Nijeriya daga cikin jerin kasashen da ta sanya wa idanu kan almundahanar kudade.

Kungiyar ta bayyana cire sunan Nijeriya ne yayin zaman da ta gudanar a hedikwatarta da ke birnin Paris na kasar Faransa a ranar Juma’a.

Google search engine

Jaridar Punch ta ruwaito shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na bayyana wannan lamari a matsayin gagarumin ci-gaba, wanda ya samo asali daga yadda gwamnatinsa ke daukar matakai wajen yakar zamba, da kuma almundahanar kudade.

Labari mai alaka: EFCC ta sa sunan Mele Kyari cikin jerin waɗanda za ta rika sa ido kansu bayan da kotu da dakatar da asusun ajiyar bankinsa

A shekarar 2023 ne kungiyar ta sanya Nijeriya cikin jerin kasashen da ta sa wa ido, sakamakon yadda ta ce ƙasar na da rauni wajen yakar wannan matsala, har ma da rashin hadin kai a tsakanin hukumomi masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Manyan Jami’an soji za su fuskanci ritayar dole bayan sauye-sauye a fannin tsaron Nijeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai manyan jami'an sojin Nijeriya  masu mukamin Janar akalla 60 da za su fuskanci ritayar dole, biyo bayan sauye-sauyen da...

Rashin gogewar siyasa ta sa ban tsayar da El-Rufa’i don ya gaje ni ba – Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya ki tsayar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa'i don ya gaje a shekarar 2007...

Mafi Shahara