Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai mai kula da gyaran kundin tsarin mulki ya amince da ƙirƙirar sabbin jihohi guda shida a Nijeriya.
Kamar yadda rahoton ya nuna, wannan shawara ta fito ne daga taron kwana biyu da aka gudanar a birnin Legas, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, da mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu.
Kwamitin ya tattauna kan ƙuduri 69, buƙatun ƙirƙirar jihohi 55, gyaran iyakokin jihohi biyu, da kuma buƙatun ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278 yayin taron.
A yayin zaman ranar Asabar, mambobin kwamitin sun amince da ƙirƙirar jihohi shida sabbi, kuma idan majalisar ta amince da wannan mataki gaba ɗaya, adadin jihohi a Nijeriya zai ƙaru daga 36 zuwa 42.


