Jam’iyyar haɗaka ta ADC ta ce za ta kai ƙorafi gaban Ƙungiyar ci-gaban kasashen yammacin Afrika ECOWAS da sauran ƙasashen duniya kan hare-haren da ake ta kai wa mambobinta a sassa daban-daban na Nijeriya.
Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, jam’iyyar ta bayyana cewa irin waɗannan hare-haren sun zama ruwan dare a jihohin da APC ke mulki, abin da ke nuna alamar ƙoƙarin murkushe jam’iyyun adawa kafin babban zaɓen 2027.
Mai magana da yawun jam’iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya zargi jam’iyyar APC da hana ƴan adawa damar bayyana ra’ayinsu, yana mai cewa hakan na iya kai ƙasar ga zaɓe mai cike da tashin hankali a shekarar 2027.


