Hukumar ba da agajin gaggawa ta Nijeriya NEMA, ta bayyana cewa ta karɓi ’yan Nijeriya 153 da suka dawo daga ƙasar Chadi, ƙarƙashin shirin Ƙungiyar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Tarayya.
Kamar yadda sanarwar ofishin NEMA na Legas ta nuna a shafin X ranar Talata, matafiyan sun iso filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas a ranar Lahadi, 27 ga Oktoba, 2025, da misalin ƙarfe 12:15 na rana, ta jirgin ASKY Airlines mai lamba CAS-AC.
Sanarwar ta ce cikin matafiyan da suka dawo akwai manya 105 (maza 63 da mata 42), yara 45 (maza 25 da mata 20), da jarirai 3, dukkaninsu mata.



