Asusun ba da bashin karatu ga ɗaliban manyan makarantu ya bayyana cewa ya raba Naira biliyan 116.4 ga ɗalibai sama da dubu 624, tun bayan ƙaddamar da tsarin neman bashin a watan Mayu, 2024.
Kamar yadda rahoton da Asusun ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata, 28 ga Oktoba, 2025, ya nuna, an karɓi buƙatu fiye da 929,000, inda ɗalibai 624,535 suka amfana, yayin da aka samu ƙarin sabbin masu neman bashi 12,398 a rahoton baya-bayan nan.
Asusun ya bayyana cewa an biya makarantu 239 Naira biliyan 65.3 a matsayin kuɗin karatu, yayin da Naira biliyan 51.1 ta shiga hannun Ɗalibai domin ciyarwa da sauran bukatun yau da kullum.



