Gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugaba Donald Trump ta soke takardar izinin shiga ƙasar ga Farfesa Wole Soyinka, sanannen marubuci a duniya.
Farfesa Soyinka ya bayyana hakan ne a taron manema labarai a birnin Lagos, a ranar Talata, inda ya ce bai san wani laifi da ya aikata da zai sa a hana shi shiga kasar ba.
A cewarsa, ofishin jakadancin Amurka ne ya sanar masa da hakan a cikin wata wasika,a cewarsa yana binciken ko akwai wani laifi da ya aikata a baya wanda ya dace da wannan hukunci, domin, a bai taba aikata laifi ko karya doka a Amurka ko a wata kasa ba.



