Majalisar wakilai ta Nijeriya ta amince da bukatar shugaban Tinubu na neman bashin dala biliyan 2.347 daga ƙasashen waje domin cike gibin kasafin kuɗin 2025 da kuma sake biyan wani tsohon bashin a Eurobond.
An amince da bukatar ne bayan rahoton kwamitin Majalisa kan tallafi da harkokin basussuka da shugaban kwamitin, Ɗan majalisa Abubakar Hassan Nalaraba, ya gabatar a zaman majalisar da kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya jagoranta.
Jaridar Punch ta rawaito cewa tun bayan da shugaba Tinubu ya hau mulki a watan Mayun 2023, gwamnatinsa ta karɓi basussuka da dama domin tallafa wa shirin gwamnati da ayyukan ci gaba.
A cikin shekaru biyu, Nijeriya ta karɓi sama da dala biliyan 7.2 daga bankin duniya da kuma bashin dala biliyan 1 daga bankin raya Afirka.



