Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan takardun afuwa da sassauta hukunci ga wasu mutane da aka taɓa yanke wa hukunci, domin aiwatar da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na yin afuwa.
Kamar yadda sanarwar fadar shugaban ƙasa ta bayyana a ranar Talata, 29 ga Oktoba, 2025, matakin ya biyo bayan tattaunawa da Majalisar Koli ta Ƙasa da kuma ra’ayoyin jama’a game da batun.
Shugaban ƙasa ya kuma bada umarnin sake nazarin jerin sunayen wadanda aka fara tsara yi musu afuwa domin tabbatar da adalci da tsaro.
Sanarwar ta ce an cire sunayen wadanda suka aikata manyan laifuka kamar sace mutane, fataucin miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, damfara, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba, daga jerin.
Wasu kuma da aka riga aka yi musu afuwa a baya, an rage musu hukunci ne kawai ba a sake su gaba ɗaya ba.
A cewar gwamnatin tarayya, wannan mataki ya zama dole saboda muhimmancin tsaron ƙasa, jin tausayin waɗanda aka yi wa laifi, da kuma girmama ƙoƙarin hukumomin tsaro.



