Fadar shugaban Nijeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu da shugaban Amurka, Donald Trump za su gana a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa domin tattaunawa kan zargin kisan Kiristoci a kasar.
Wannan na zuwa ne bayan kalaman Trump da suka zargi gwamnatin Nijeriya da rashin daukar mataki kan hare-haren da ake kai wa Kiristoci, inda ya kuma yi barazanar kai hari a Nijeriya da kuma dakatar da tallafin Amurka.
Mai ba shugaban kasar shawara Mr Daniel Bwala ya ce shugabannin biyu na da kyakkyawar alaka wajen yaki da ta’addanci, inda ya kara da cewa gwamnatin Trump ce ta amince da sayar wa Nijeriya makamai, kuma gwamnatin Tinubu ta yi amfani da damar wajen samun gagarumar nasara a yaki da ta’addanci.



