Gwamnonin Arewa 12 da wasu sarakunan gargajiya da ma wasu manyan alkalai sun shiga cikin wata sabuwar ce-ce-ku-ce ta diflomasiyya bayan Majalisar dokokin Amurka ta fara nazarin wani kudiri da zai iya sanya musu takunkumi.
Amurka ta na zarginsu da hannu a kisan kiyashi kan Kiristoci da cin zarafi ta hanyar dokokin shari’a da batun raina addini a Nijeriya.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasa mai damuwa ta musamman tare da umartar sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio da ya dauki mataki cikin lokaci.
Kudirin da Sanata Ted Cruz ya dauki nauyi, mai suna “Nigeria Religious Freedom Accountability Act 2025”, yana neman sanya takunkumi kan manyan jami’an gwamnati, sarakuna, da alkalai da ake zargi da amincewa ko tallafawa cin zarafi kan Kiristoci da sauran ƙananan ƙungiyoyin addini kamar yadda jaridar punch ta ruwaito.
Idan aka amince da kudirin, za a iya sanya musu takunkumin hana visa, toshe asusun banki da sauran takunkumin kudi bisa tsarin dokar Global Magnitsky, musamman ga gwamnonin jihohi 12 da suka aiwatar da dokar Shari’a mai cike da sabani a tsakanin Kiristoci da Musulmi.



