DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rikicin PDP na kara yin kamari yayin da bangarorin Damagum da Anyanwu ke shirin shiga ofishin jam’iyyar a lokaci guda

-

Da yiyuwar kara samun rikici a jam’iyyar PDP yayin da bangarorin shugaban jam’iyya Umar Damagum da sakatare Samuel Anyanwu ke shirin komawa aiki a ofishin jam’iyyar na kasa da ke Wadata Plaza, Abuja, a yau Litinin.

A ranar Asabar, bangaren Damagum ya gudanar da taro a Legacy House da ke Maitama, yayin da bangaren Anyanwu kuma ya yi nasa taron a ofishinsa da ke Wuye a Abuja.

Google search engine

Wata majiya daga jam’iyyar ta shaida wa Daily Trust cewa duka bangarorin biyu na shirin yin aiki a ofishin jam’iyyar guda, abin da ke haifar da fargaba a tsakanin ma’aikata na jam’iyyar.

Majiyar ta kara da cewa bangaren Nyesom Wike na kokarin jan hankalin wasu mambobin kwamitin gudanarwa domin samun rinjaye a cikin jam’iyyar, lamarin da zai iya haddasa sabon rikici idan duka bangarorin suka hadu a ofishin a yau.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ba a take hakkin Kiristoci a Nijeriya ba – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya Janar Olufemi Oluyede ya karyata ikirarin cewa ana zaluntar Kiristoci a Nijeriya, inda ya ce babbar matsalar Nijeriya ita ce ta’addanci. Janar...

Ya kamata ka taka wa Matawalle burki – Jam’iyyar PDP ta shaida wa Tinubu

Kungiyar dattawan Arewa ta jam’iyyar PDP ta zargi ministan tsaron Nijeriya, Bello Matawalle, da jagorantar sauya shekar da dama daga PDP zuwa APC ta hanyar...

Mafi Shahara