Gwamnatin kasar China ta nuna goyon bayanta ga Shugaba Bola Tinubu, tana mai gargadi ga kowace kasa da ke tsoma baki cikin harkokin cikin gidan Nijeriya.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Mao Ning, ta bayyana haka ne a martani ga barazanar shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya zargi gwamnatin Nijeriya da kisan Kiristoci.
Trump ya ce zai dauki matakin soja da kuma katse tallafin Amurka idan gwamnatin Tinubu ta kasa shawo kan matsalar, amma kasar China ta ce irin wannan barazana ba ta dace da dangantakar kasa da kasa ba.
Mao Ning ta kara da cewa Sin na goyon bayan Nijeriya wajen tafiyar da mulkinta bisa tsarin da ya dace da yanayin kasar, tare da yin watsi da duk wani yunkurin amfani da addini a matsayin dalilin tsoma baki kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa.



