Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya gargadi cewa ci-gaban tattalin arzikin Nijeriya ba ya fassaruwa zuwa ingantacciyar rayuwa ga ’yan ƙasar.
Sanusi ya bayyana hakan ne a wani taron kasa da kasa na Afirka kan kudin Musulunci da aka gudanar a Legas, inda ya ce ƙididdigar ci-gaban tattalin arziki da hauhawar farashi ba su nuna ainihin halin da talakawa ke ciki ba.
A cewarsa, duk da cewa GDP na ƙaruwa, idan ya takaita ne ga wasu kawai, yawancin jama’a za su ci gaba da fama da talauci.
Sanusi ya shawarci cibiyoyin kuɗin Musulunci da su mai da hankali wajen tallafawa kananan ’yan kasuwa, manoma da ma’aikata a yankunan karkara, yana mai cewa hakan ne kaɗai zai tabbatar da ingantacciyar rayuwa ga jama’a.



