Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasar Portugal, Cristiano Ronaldo, ya bayyana cewa zai yi ritaya daga wasa nan ba da jimawa ba, yana mai cewa abu ne mai wahala kawo ƙarshen kyakkyawar rayuwarsa ta wasa. Ya bayyana haka ne a wani shirin tattaunawa da aka watsa a Burtaniya.
Ronaldo, wanda yanzu ke bugawa Al Nassr ta Saudiyya, shi ne mafi yawan zura kwallo a tarihin ƙwallon ƙafa da kwallaye 952 ga ƙungiyoyi da ƙasa. Kwanan nan ya ce yana fatan kai kwallaye 1,000 kafin ya ajiye takalman sa.
Ronaldo ya ce, tuni ya fara shirin rayuwa bayan ƙwallo tun yana da shekara 25 zuwa 27 kuma zai yi ritaya ne domin mai da hankali kan iyalinsa da tarbiyyar ’ya’yansa.
A cewarsa, har yanzu yana bibiyar tsohuwar ƙungiyarsa ta Manchester United duk da yadda ya bar kulob ɗin cikin rashin jituwa amma ya damu da halin da kungiyar ke ciki, domin kulob ɗin yana da tarihin ban mamaki kuma har yanzu yana da matsayi a zuciyarsa.



