Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa gwamnatin Amurka ta yi kuskuren fahimtar hakikanin matsalolin tsaro a kasar.
Ministan yada labaran Nijeriya, Mohammed Idris, ya ce gwamnatin Nijeriya ta damu da yadda Amurka ta yi hanzarin fitar da wannan matsayi bisa bayanan da ba su da tushe. Ya ce matsalolin tsaro a Nijeriya sun shafi Musulmai da Kiristoci baki É—aya, ba wai rikicin addini ba ne.
DCL Hausa ta ruwaito cewa Ministan ya jaddada cewa rikicin manoma da makiyaya a Plateau da Benue ya samo asali daga tsoffin matsaloli da canjin yanayi da fari suka haifar da ƙara taɓarɓarewar. Ya ƙara da cewa gwamnati tana ƙarfafa haɗin kai da ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, don kawo ƙarshen ta’addanci a yankin Sahel da Nijeriya baki ɗaya.
A cewarsa, hadin gwiwar da ke tsakanin Nijeriya da Amurka ya haifar da samun jiragen Super Tucano da ake amfani da su a yaƙin ta’addanci, tare da shirin karɓar sabbin jiragen yaƙi na AH-1Z Viper domin ƙarfafa rundunar sojojin sama.
Hakazalika, ya ce gwamnatin Tinubu tana bin duk hanyoyin diflomasiyya da siyasa don gyara kuskuren fahimtar da gwamnatin Amurka ta yi, tare da tabbatar da cewa ’yancin addini da rayuwar kowane ɗan ƙasa za su kasance a ƙarƙashin kariya da doka.



