Rundunar ‘yan sandan jihar Edo ta kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27 bisa zargin shirya garkuwa da kanta don karɓar kudin fansa daga mijinta.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikoedem, ta ce mijin Chioma, Paul Adaniken, ya kai rahoto cewa matarsa da ɗansa sun ɓace, inda daga baya aka kira shi da wata lamba da ba a sani ba ana neman fansar Naira miliyan bitar.
Bincike ya gano cewa ɗan’uwan matar, Osita Godfrey, da wani abokinsu Martins Chidozie, sun taimaka wajen shirya satar. Daga baya Chioma ta amsa cewa ita ce ta tsara komai don ta karɓi kuɗi daga mijinta.
‘Yan sanda sun ce an kwato kudin fansar kuma an mika lamarin ga sashen binciken manyan laifuka na jihar don ci-gaba da bincike da gurfanarwa.



