Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatinsa na kawar da ta’addanci da kuma karfafa dangantaka tsakanin Nijeriya da abokan hulɗarta na duniya.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis kafin zaman majalisar zartarwa na kasa da aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja, zama na farko tun watan Yuli.
A cewarsa, ana tattaunawa da kasashen duniya ta hanyar diflomasiyya, kuma ya tabbatar da cewa za a murkushe ta’addanci.
Jawabin Tinubu ya zo ne kwanaki bayan shugaban Amurka Donald Trump ya sanya Nijeriya cikin jerin “Kasashen da ke da damuwa ta musamman,” abin da gwamnatin Nijeriya ta ce ba daidai ba ne wajen bayyana hakikanin matsalar tsaro.
Hakazalika Tinubu ya ce gwamnatinsa na ci-gaba da tattaunawa da kasashen duniya domin tabbatar da tsaro, zaman lafiya, da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.



