DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar alhazan Nijeriya ta kammala duba gidajen saukar alhazai a Madina don aikin hajjin 2026

-

Hukumar alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta bayyana cewa ta kammala duba wuraren saukar alhazai da masu samar da abinci a birnin Madina a cikin shirin farkon da take yi na gudanar da aikin hajji na shekarar 2026.

Wannan bayani na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban hukumar ta fuskar yada labarai, Ahmad Muazu, ya fitar a ranar Juma’a.

Google search engine

A cewar Muazu, kwamitin ya duba sama da otal 20 da wuraren dafa abinci guda bakwai a yankin markaziyya, inda suka tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro, tsafta da sharuddan hukumar.

Hukumar ta NAHCON ta bayyana cewa za ta cigaba da tabbatar da cewa dukkan alhazai daga Nijeriya suna samun ingantaccen ayukka da ya dace da kuɗin da aka biya, tare da ƙarfafa tsare-tsaren da ke tabbatar da gaskiya da inganci wajen hidimomin aikin Hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar wakilan Nijeriya ta yi Alla-wadai da harin da aka kai ma dan majalisa a jihar Neja

Majalisar Wakilan Nijeriya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa tawagar dan majalisa Jafaru Mohammed Ali, wanda ke wakiltar mazabar Borgu/Agwara ta Jihar...

Muna bibiyar barazanar hari da Amurka ke yi ma Nijeriya sau da kafa – Gwamnatin Rasha

Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa tana sa ido sosai kan rahotannin da ke nuna yiwuwar Amurka ta kai farmaki a Nijeriya, kamar yadda mai magana...

Mafi Shahara