Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan dokar kafa kwalejin kimiyya da fasaha “Gaya Polytechnic” a wani mataki na fadada damar samun ilimin gaba da sakandare tare da inganta koyon sana’o’in zamani a fadin jihar.
Mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana haka ne bayan rattaba hannun da ya samu halartar shugaban majalisar dokoki ta jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, da mataimakin shugaban majalisar, Hon. Muhammad Bello Butubutu, wadanda suka mika kudirin.
Gwamnan ya ce sabuwar kwalejin za ta bai wa matasa damarmaki na koyon horo da fasaha da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki, kuma wannan shine burin gwamnati wajen fadada harkokin ilimi a fadin jihar Kano.



