Jam’iyyar PDP mai hamayya a Nijeriya ta bayyana korar ministan birnin Abuja Nyesom Wike da wasu ‘ya’yanta daga cikinta.
Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin kudancin Nijeriya Cif Olabode George ne ya gabatar da kudurin korar yayin babban taron jam’iyyar da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.
Baya ga ministan Abuja Nyesom Wike, jam’iyyar ta kori tsohon sakatarenta Samuel Anyawu da tsohon gwamnan Ekiti Ayodele Fayose kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.



