Wani rahoto ya nuna cewa likitoci 4,193 ne suka fice daga Nijeriya don neman rayuwa mai inganci a shekarar 2024.
Labari mai alaka: Likita daya na duba marasa lafiya 9,083 in ji kungiyar likitoci a Nijeriya
Rahoton wanda ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar, ya kuma yi nuni da cewa jimillar likitoci, masu aikin jinya, kwararru a fannin magunguna da kuma masu gwaje-gwaje 43,221 ne suka fice daga ƙasar a tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Kazalika ya yi gargaɗin cewa karuwar ficewar kwararrun na iya zama babbar barazana ga fannin lafiya na kasar, inda ya yi nuni da muhimmancin kyautata rayuwarsu don ganin sun ci gaba da zama a Nijeriya tare da gudanar da ayyukan su yadda ya dace.



