Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriya NDLEA, Janar Buba Marwa (rtd), ya bayyana cewa wa’adinsa na biyu zai zama mafi tsauri ga duk masu hada-hadar kwayoyi a fadin ƙasar.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai na hukumar, Femi Babafemi, ya fitar a Abuja ranar Asabar, Marwa ya yi wannan gargadi ne yayin da ya koma ofis bayan sake nada shi da Shugaba Bola Tinubu a ranar 14 ga Nuwamban 2025.
Marwa, yayin da yake jawabi ga daruruwan ma’aikata da suka taru domin taya shi murna, ya ce sabon wa’adin na shi zai zama mai matukar kunci ga dilolin miyagun kwayoyi.



