Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun halaka wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Zamfara, Alhaji Umar Moriki da safiyar ranar Asabar.
Gidan talabijin na Channels, ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe, kusa da garin Fegi a karamar hukumar Tsafe, yayin da Marigayin ke tafiya daga Gusau zuwa Kaduna.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran APC a jihar Zamfara Yusuf Idris ya fitar, jam’iyyar ta bayyana rasuwar Marigayi Moriki a matsayin babban rashi, inda ta ce ya halarci taron shugabannin jam’iyya da karamin ministan tsaro Bello Matawalle ya jagoranta kafin aukuwar harin.
Marigayi Moriki ya taɓa rike mukamai da dama, ciki har da mataimakin shugaban karamar hukumar Zurmi da mai bai wa gwamna shawara kan hasken wutar lantarki a yankunan karkara, kazalika ya yi takarar kujerar majalisar wakilai ta Zurmi/Shinkafi a zaben 2023.



