’Yan bindiga sun hallaka mutane uku tare da sace akalla 64 a Fegin Baza da ke Tsafe, jihar Zamfara. Mata da yara na cikin wadanda aka yi garkuwa da su, sannan mutane hudu sun jikkata.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, daga cikin wadanda aka kashe har da jigo a jam’iyyar APC, Umaru Moriki, wanda aka harba a kan hanyar Gusau zuwa Tsafe. Shaidun gani da ido sun ce maharan sama da 30 ne dauke da bindigogi a kan babura.
Harin ya faru kwana guda bayan ziyarar ministan tsaro Bello Matawalle, wanda ya sanar da turo sabbin sojoji tare da alkawarin murkushe ’yan bindiga.
Zamfara na ci-gaba da fama da hare-hare a kauyuka da hanyoyi, lamarin da ya tilasta dubban mutane barin gidajensu bayan garkuwa, kashe-kashe da barna sun yi kamari.



