Bangaren jam’iyyar PDP da ke goyon bayan ministan Abuja, Nyesom Wike, ya sanar da cewa za a gudanar da taron gaggawa na kwamitin amintattu da na zartaswa na jam’iyyar a ranar Talata, 18 ga watan Nuwamba, 2025, a hedikwatar jam’iyyar da ke Wadata Plaza, Abuja.
A cikin sanarwar da sakataren Jam’iyyar na bangaren Wike, Samuel Anyanwu, ta nuna wadda mai taimakawa ministan wajen yada labarai, Lere Olayinka, ya wallafa, taron amintattun zai fara da misalin 11 na safe, yayin da na zartaswa zai biyo baya da karfe 2 na rana.
Sanarwar ta ce halartar manyan jiga-jigan jam’iyyar yana da muhimmanci domin tattaunawa kan muhimman batutuwa, musamman bayan da PDP a taronta na kasa da aka yi a Ibadan ta kori Wike, Anyanwu, Ayo Fayose, Kamaldeen Ajibade da wasu shugabanni bisa zargin cin amanar jam’iyya.
Korarsu ta biyo bayan kudirin da Bode George ya gabatar, Samaila Buga na PDP Bauchi ya mara wa baya, sannan gwamna Bala Mohammed ya sanya wa kwamitin muryar amincewa wadda ta nuna sahalewar wakilai kan hukuncin share baragurbin cikin jam’iyyar.



