Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu ya bayyana cewa manufofin tattalin arziki da na gyare-gyaren hukumomin gwamnati suna nufin bai wa matasa kwarewa da ilimi mai inganci domin su iya fafatawa a duniya da kuma tabbatar da makomarsu ta hanyar ci-gaban ilimi.
Tinubu ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin yayin da yake karbar Duke na Edinburgh, Prince Edward, a Fadar shugaban Nijeriya, Abuja kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A cewarsa, batun matasa zai kasance gaba-gaba a taron G-20 da za a gudanar wannan makon, inda ya kara da cewa manufofin gwamnati sun mayar da hankali kan yawan jama’a da bunkasa kwarewa don habaka tattalin arziki.
Hakazalika, ya jaddada cewa sabon shirin bayar da rancen dalibai wani muhimmin mataki ne na fadada damar samun ilimi ga matasa, inda ya ce gwamnati na amfani da kyawawan dabaru wajen samar da kwarewa a fannoni da dama, domin inganta rayuwar matasa da ci-gaban kasa.



