DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnati ta binciki ta’azzarar matsalar tsaro a Nijeriya – Kwankwaso

-

Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta da gudanar da bincike kan musabbabin ta’azzarar matsalar tsaro a wasu sassan kasar.

 

Google search engine

Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya yi Allah-wadai da sace ‘yan makaranta 25 da ‘yan bindiga suka yi a jihar Kebbi, bayan farmakin da suka kai.

 

Kazalika Kwankwaso ya nuna damuwa da sauran matsalolin tsaro da ke faruwa a jihohi irin su Zamfara da Kano, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

 

A hannu guda, ya bayyana kisan Birgediya Janar Musa Uba a Borno a matsayin wani bakin tabo a fagen tsaron Nijeriya, yana mai bukatar a gaggauta bincikar lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

El-Rufai ya zargi gwamnatin Tinubu da hannu a yunƙurin sanya Kwankwaso cikin jerin takunkumin Amurka

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya kasancewa a bayan yunƙurin dan Majalisar Dokokin Amurka,...

Shehu Sani ya karyata El-Rufai kan batun bacewar Dadiyata

Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Comrade Shehu Sani, ya karyata ikirarin tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, cewa Abubakar Idris wanda aka fi sani da...

Mafi Shahara