Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya(NERC) ta bayyana cewa an yi asarar wutar lantarki da ta kai Naira biliyan 40.61 a layukan ba da lantarki, wacce bata kai ga cibiyoyin rarrabawa ba.
Lamarin ya faru ne duk da ƙarancin lantarkin da ake samu a gidaje da kamfanoni a fadin ƙasar, in ji rahoton jaridar Daily Trust.
A cewar rahotannin da hukumar ta fitar na kwata-kwata, kamar yadda jaridu suka ruwaito, an yi asarar biliyan N22.64 a rubu’i na farko na 2025, yayin da asarar ta kai biliyan N17.97 a rubu’i na biyu.
Hukumar ta bayyana wannan a matsayin Transmission Loss Factor (TLF), wato kaso na wutar da masana’antar samarwa ta tura amma ta salwanta a hanya ko kuma aka yi amfani da ita a tashoshi, ba tare da ta kai ga kamfanonin rarrabawa ko ƙasashen waje ba.
Rahoton ya nuna cewa adadin da aka yi asara ya zarce kashi 7 cikin 100 da aka amince, inda aka samu kashi 9 cikin 100 na salwantar wutar a kwata na farko, abin da ya nuna raguwar ingancin tsarin watsawa.



