Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce matsalar tsaro ita ce babbar damuwar Nijeriya, musamman Arewacin ƙasar, yana mai cewa dole a hanzarta dawo da zaman lafiya da haɗin kai.
Da yake magana a Kaduna ta bakin Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a bikin cika shekara 25 na kungiyar tuntuba ta Arewacin Nijeriya, ACF, ya ce gwamnati na aiki da hanzari don murkushe ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke lalata tattalin arziƙi da ilimi.
A cewarsa, babu abin da ke tayar masa da hankali irin matsalolin tsaro musamman a Arewacin kasar inda ya ce ba za a ci-gaba ba matukar wani bangare na kasar na cikin matsala kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Tinubu ya ce gwamnatinsa ta gaji matsaloli masu tsanani amma tana tunkararsu, yana fatan Arewacin Nijeriya za ta farfaɗo tare da manyan ayyuka kamar titin Abuja–Kaduna–Kano da kuma rijiyar mai ta Kolmani da ake sa ran za su farfado da tattalin arziƙi.
Hakazalika, Tinubu ya yaba wa ACF bisa zama murya ɗaya ta Arewa, yana gargadin cewa yankin ba zai ci-gaba ba idan shugabanni suka kasa kare marasa ƙarfi, musamman yayin da jama’a ke fama da tsoro da yunwa.



