Ma’aikatar Ilimi ta Nijeriya ta musanta wani saƙon da yake yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an ba da umarnin rufe makarantu a fadin ƙasar daga 24 ga watan Nuwamba, 2025.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta fitar a ranar Asabar, ta ce labarin ba gaskiya ba ne, kuma ba daga gwamnatin tarayya ko ta jiha, ko wata hukuma ta tsaro da aka amince da ita yake ba.
Sanarwar ta bukaci jama’a su dogara kacokan ga bayanai daga ingantattun hanyoyin gwamnati kawai, tare da gargaɗin cewa duk wani saƙo daga majiyoyi marasa tushe ya kamata a yi watsi da su domin hana yaɗa bayanan ƙarya.
Ma’aikatar ta ce bayanai daga gwamnatin tarayya, ma’aikatar ilimi ta tarayya, gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro ne za su iya zama a hukumance kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Sanarwar ta zo ne kwana daya bayan gwamnatin tarayya ta rufe manyan makarantu 41 da ke cikin yankunan da ke fuskantar tashin hankali, sannan wasu jihohi kamar Kwara, Filato, Katsina da Neja suma sun dakatar da karatu saboda matsalar tsaro.
A baya-bayan nan ma, gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya umarci duk makarantu su daina kwana da ɗalibai a makarantu har sai yadda hali ya ba da.



